A yau, fasahar wucin gadi (AI) tana kara saukaka rayuwar mutane ta fannoni da dama, ciki har da samar da bidiyo daga rubutu wato text-to-video. Wannan na nufin zaka iya rubuta labari ko bayanai, sannan AI ta kirkiri bidiyo daga ciki ba tare da ka dauki hotuna ko daukar lokaci wajen editing ba.
Mataki-Mataki Yadda Ake Yin Text to Video
1. Zabi Platform Din da Kake So Ka Yi Amfani da Shi
Akwai wasu shahararrun AI tools da suke taimakawa wajen kirkirar video daga rubutu kamar haka:
Pictory (pictory.ai)
Lumen5 (lumen5.com)
InVideo (invideo.io)
Synthesia (synthesia.io)
HeyGen (heygen.com)
2. Create Account (Idan ya zama dole)
Yawancin wadannan platforms suna bukatar ka yi sign up kafin ka fara amfani da su. Zaka iya amfani da email ko Google account.
3. Rubuta Rubutunka ko Zabi Script
Ka tsara rubutun da kake son ya zama video. Misali:
> "Wannan bidiyon yana bayani akan yadda ake dasa tumatir a gonar zamani..."
Rubutun ya zama mai sauki kuma kai tsaye.
4. Shigar da Rubutun a Cikin AI Tool Din
Daga nan, zaka danna “Create Video” ko wani abu makamancin haka, sannan ka liƙa rubutunka.
AI zata fara kirkirar scenes da media clips masu dacewa da rubutunka.
5. Daidaita Style, Voice, da Background Music
Zaka iya zabar:
Nau’in murya (masculine ko feminine)
Salon bidiyon (formal, cinematic, vlog, da sauransu)
Wakokin baya da kuma launuka
6. Duba Video, Gyara Idan Akwai Bukata
Bayan an gama, zaka iya duba bidiyon domin ganin ko ya dace da abin da ka tsara. Idan akwai gyara, zaka iya canza rubutu ko scene.
7. Sauke (Download) ko Share
Idan ka gamsu da bidiyon, zaka iya sauke shi ko kuma ka tura kai tsaye zuwa YouTube, Facebook, Instagram, da sauransu.
---
Amfanin Yin Text to Video Da AI
Ajiyar lokaci
Inganci
Dacewa da social media content
Sauƙin sarrafawa
---
Related Search 🔎
Yadda ake samar da video daga AI
AI text to video tutorial Hausa
Pictory ai yadda ake amfani
Lumen5 Hausa tutorial
Invideo yadda ake rubuta video
Sauya rubutu zuwa bidiyo
AI video generation in Hausa
Best AI video creator tools 2025
Hanyoyin kirkirar video da AI
Yadda ake amfani da AI wajen kirkirar bidiyo
1 Comments
Barka
ReplyDelete