A wannan zamanin na ci gaban fasaha, samun hotuna masu kyau da kayatarwa ba sai ka ɗauki hoto da kyamara ko haya graphic designer ba. Tare da wayarka kawai, zaka iya amfani da fasahar Generative AI don ƙirƙirar hotuna cikin sauƙi. Wannan yana da matuƙar amfani ga masu kasuwanci da ke son tallata hajarsu cikin salo da tasiri.
Menene Generative AI?
Generative AI wata fasaha ce da ke amfani da artificial intelligence domin ƙirƙirar sabbin abubuwa daga bayanan da mutum ya bayar. Wannan zai iya haɗawa da hotuna, bidiyo, rubuce-rubuce, da sauransu. A wannan rubutu, zamu mayar da hankali ne akan yadda zaka ƙirƙiri hotuna daga rubutu (text) ta hanyar wayarka.
Yadda Zaka Yi Amfani da Wayarka
Ga matakai masu sauƙi da zaka bi:
1. Zazzage App na Generative AI
Ga wasu shahararrun apps da zaka iya amfani da su:
Canva (Magic Media tool)
Remini AI Photo Enhancer
Picsart AI Image Generator
Bing Image Creator
Imagine AI Art Generator
StarryAI ko Artbreeder
2. Rubuta Bayani (Prompt)
Bayan ka buɗe app ɗin, zaka ga wani fili da zaka rubuta irin hoton da kake so. Misali:
> “Hoto na mace sanye da kayan gargajiya tana tsaye a kasuwa”
AI zai fahimta ya ƙirƙiri hoto daidai da bayanin.
3. Sauke Hoton
Bayan hoton ya bayyana, zaka iya sauke shi zuwa wayarka. Zaka iya amfani da shi wajen:
Ƙirƙirar flyer
Sanya shi a tallanka
Wallafa a social media
Yin amfani da shi a website ɗinka
Fa’idodin Amfani da Generative AI Ga Kasuwanci
Tallata Kaya: Zaka iya ƙirƙirar hotuna masu kyau don jawo hankalin abokan ciniki.
Samun Unique Content: Hoton da babu kamar shi a duniya.
Rage Kuɗin Aiki: Ba sai ka biya mai ɗaukar hoto ko graphic designer ba a wasu lokuta.
Ƙarfafa Alamar Kasuwanci (Brand): Yin aiki da hotuna masu ɗaukar hankali daidai da salo da launin kasuwancinka.
#malamiromba #30dayschallenge #30dayscreativity #Hausa #arewa
0 Comments