Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano ta buɗe ƙofar daukar sabbin ma’aikata, inda take gayyatar ‘yan asalin jihar da suka cancanta su cike guraben aiki daban-daban a hukumar.
Wannan bayani ya fito ne daga shafin hukumar a ranar Litinin, inda aka bayyana cewa shirin na daga cikin matakan da gwamnatin Kano ke ɗauka don ƙarfafa aikin hukumar da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana a fadin jihar.
Abubuwan Da Ake Bukata:
-
Dole ne mai nema ya kasance ɗan asalin jihar Kano
-
Dole ne ya mallaki Lambar Shaidar Ƙasa (NIN) da BVN
-
Shekarunsa su kasance tsakanin 25 zuwa 30 kafin ranar 30 ga Afrilu, 2025
-
Dole ne ya kasance lafiya jikinsa da kwakwalwarsa, kuma bai taɓa samun hukuncin kotu ba
Kwarewar Karatu da Takardun da Ake Bukata:
-
SSCE/NECO/GCE – sai an samu ƙididdiga biyar ciki har da Lissafi da Turanci
-
OND, NCE, HND ko Digiri (Bachelor’s Degree) a fannonin da suka dace
-
Takardar NYSC ko ta exemption ga masu digiri
Guraben Aiki:
-
Assistant Investigator (GL 06) – Ga masu OND ko ND
-
Investigator (GL 07) – Ga masu NCE ko Advanced Diploma
-
Superintendent II – Ga masu HND ko Digiri
Sanin amfani da kwamfuta musamman Microsoft Office yana da muhimmanci. Wanda ke da ƙwarewa a kayan aiki na sarrafa bayanai (data tools) zai fi samun dama.
Lokacin Cike Aikace-aikacen:
-
Fara cike fom: Litinin, 7 ga Afrilu, 2025
-
Rufewa: Karfe 12 na dare, Lahadi, 13 ga Afrilu, 2025
Hukumar ta bayyana cewa ba za ta karɓi takardu a hannu ba, kuma kawai wadanda suka samu nasara za a tuntuɓa.
Wannan shirin na daukar aiki yana daga cikin manufofin cigaban jihar Kano, tare da shirin haɗin gwiwa da jihar Georgia ta Amurka don bunkasa wasu sassa na tattalin arziki da shugabanci.
0 Comments